Kamfanin dillancin labaran kasar Iran IRNA ya rawaito Mr. Amano na cewa mahukuntan na Iran, na nuna matukar himma game da yunkurin cimma burin da aka sa gaba tsakanin sassan biyu. Daga nan sai Amano ya yi fatan za a kai ga warware dukkanin batutuwa da ke da sarkakiya don gane da shirin nukiliyar kasar.
Yayin dai wannan ziyara Amano ya zanta da shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, wanda bayan ganawar tasu ya sake jaddada muhimmancin da kasar sa ke dorawa game da warware matsalar Nukiliyar ta cikin lumana.
Ya ce Iran na ci gaba da shawarwari da masu ruwa da tsaki da kuma IAEA, ba ta kuma burin sarrafa makamashin nukiliya sama da bukatar da ta wuce ayyukan inganta rayuwar fararen hula.
Rouhani ya kara da cewa Iran na fatan a kai ga warware ragowar muhimman batutuwan da suka jibanci hakan a kasa da shekara guda. Hakan ne ma ya sa a cewar shugaba Rouhani, Iran ta ba da damar duba shirye-shiryenta game da nukiliya. Sai dai shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa, hakan zai ci gaba da kasancewa ne karkashin hurumin dokar dakile yaduwar makaman nukiliya ta MDD.
Bugu da kari shugaba Rouhani ya ce batun makaman kasar masu linzami, ba sa cikin batutuwan da za a tattauna a kan su.