141124-ebola-za-ta-iya-haddasa-matsalar-yunwa-a-yammacin-afirka-bello
|
Sanin kowa ne cewa, Ebola cuta ce mai hadari wadda za ta iya illa ga jikin dan Adam har halaka shi cikin 'yan kwanaki kadan. Sai dai a wani bangare na daban, yadda cutar take mummunan tasiri ga tattalin arziki da aikin gona shi ma zai iya yin barazana ga al'umma, musamman ma wadanda suke yammacin Afirka.
A ranar 11 ga watan nan da muke ciki, Hilal Elver, jami'ar MDD mai kula da batun kare hakkin dan Adam da samar da abinci, ta sanar da cewa, tuni annobar Ebola ta sanya wasu wuraren dake yammacin Afirka dab da fuskantar matsalar yunwa. A cewar Hilal, yawan jama'ar dake bukatar samun tallafin abinci a yammacin Afirka ya zarce miliyan 1 sakamakon annobar da ta ki ci ta ki cinyewa.
Dalilin da ya sa hakan shi ne, domin aikin gona ya kasance daya daga cikin gishikan tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, inda kashi 2 cikin 3 na al'ummar yankin ke dogara da shi, amma a wannan karo, bazuwar cutar Ebola ta haifar da babbar illa ga sha'anin noma.
Dangane da mummunan tasirin da annobar ta yi wa aikin gona, Kanayo Nwanze, shugaban asusun raya aikin gona na MDD, ya yi cikakken bayani yayin da yake hira da manema labaru a kwanakin baya, inda ya ce, a wasu kasashen dake yammacin Afirka wadanda suka fi jin radadin annobar Ebola kamarsu Guinea, Laberiya, da Saliyo, yadda jama'a suke tsananin tsoron kamuwa da cutar Ebola ya sanya gonaki yanzu su zama tamkar saura, kana aikin shuke-shuke da dashe-dashe sun katse baki daya,yayin da farashin abinci ya yi tashin zabo.
A kasar Laberiya, wurin da matsalar ta fi damunsa shi ne gundumar Lofa mai albarkatun gonaki, inda hauhawar farashin kayayyakin, da suka hada da kayan abinci, ta karu zuwa kashi 75% daga 30% a watan Augustan bana kadai. Ban da haka, a nasa bangare, ministan kula da aikin gona da samar da abinci na kasar Saliyo, mista Joseph Sam Sesay, ya ce kashi 40% na manoman kasar sun riga sun daina zuwa gona, sakamakon bazuwar annobar Ebola a kasar.
Sai dai mummunan tasirin cutar Ebola bai tsaya ga nan ba kawai, wasu abubuwa sun kara tsananta yanayin da ake ciki na karancin abinci a yammacin Afirka, wadanda suka hada da dakatar da ayyukan kwastam, da raguwar harkokin cinikayya, da rashin samun jari daga kasashen ketare, da dai makamantansu. An ce, tun bayan da cutar Ebola ta barke a kasashen Laberiya, Guinea da Saliyo, jiragen ruwan dakon kaya a tashohin jiragen ruwan wadannan kasashe suka dakatar da ayyukansu. Ko wadanda suka yarda su je tashohin, sai da aka biya su kudi mai tsadar gaske. Hakan ya sa wadannan kasashe suka kasa shigo da isassun hatsin da ake bukata daga kasashen waje, lamarin da ya kara daga farashin hatsi a wadannan kasashen.
Alkaluman da hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayar,sun nuna cewa, tun lokacin da cutar ta Ebola ta barke a kasar Guinea a watan Maris na bana zuwa wannan lokaci,cutar ta yi sanadiyar rayukan mutane fiye da 5000, yayin da mutanen da suka kamu da cutar suka zarce 14000. Sakamkon wannan yanayi mai tsanani da ake ciki ya sa masu binciken al'amuran yau da kullum suka bayyana annobar Ebola a matsayin babbar matsalar dake addabar al'ummar kasashe daban daban musamman ma a fannin kiwon lafiya. Sai dai a cewarsu, yayin da gamayyar kasa da kasa suke kokarin shawo kan annobar, ya kamata su mai da hankali kan matsalar yunwa da ke kokarin kunno kai, gami da taimakawa kasashen dake yammacin nahiyar Afirka wajen ganin an magance wannan matsala. In ba haka ba, wasu kasashen dake yankin za su kara tsunduma cikin mawuyacin hali a fannin jin kai, in ji wadannan masanan. (Bello Wang)