Mr. Ban wanda ya bayyana hakan bayan ganawarsa da shugaban bankin duniya Kim Jim-Yong, da babbar sakatariyar hukumar kiwon lafiyar ta WHO Margaret Chen da ma wasu manyan jami'ai, ya kara da cewa an samu matukar ci gaba a fannoni da dama, a wasu yankunan da aka gudanar da manufofin yaki da cutar ta Ebola. Sai dai bambacin yanayin yaduwar cutar a yankuna daban daban, da yaduwar cutar a kasar Mali, ya sa ana dada nuna matukar damuwa.
Wannan dalili ne a cewarsa ya sanya shi aikewa da Margaret Chen da wasu masana zuwa Mali, domin tattaunawa kan yadda za a kai ga dakile yaduwar cutar a kasar. Kaza lika babban sakataren MDDr ya bukaci cibiyar kula da harkokin cutar Ebola ta MDD, da ta kafa wani ofis na musamman a kasar Mali.
A nata bangare, Margaret Chen ta bayyana cewa, duk da cewa akwai yiwuwar kawo karshen yaduwar cutar Ebola a wasu yankunan yammacin Afirka, akwai bukatar ci gaba da kandagarkin yaduwar cutar a dukkanin nahiyar. (Maryam)