Na'urar bincike dake da manufar yin rigakafin cutar Ebola a yankin Kouremale, birnin dake kan iyaka tsakanin Mali da Guinea, na da inganci, a cewar faraministan kasar Mali, Moussa Mara, bayan ya kai ziyara aiki a wannan yanki a ranar Lahadi, a cewar wata majiya mai tushe.
A birnin Kouremale mai nisan kilomita 127 da birnin Bamako, kana kuma babbar hanyar shige da fice tsakanin kasashen biyu ne aka fara gano mutumiya ta farko mai dauke da cutar Ebola da ta shigo kasar Mali, kuma wata karamar yarinya ce 'yar shekaru biyu da cutar ta kashe a cikin watan Oktoba. A cewar sanarwar fadar faraministan kasar Mali, matakin da aka dauka a Kouremale na da inganci sosai, kuma na'urar tana aiki a ko da yaushe. (Maman Ada)