in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mummunan mafarkin gasar cin kofin duniya ya shude in ji Guedes
2014-09-19 10:15:22 cri
Tsohon dan wasan gaban kungiyar kwallon kafar kasar Brazil Frederico Chaves Guedes, ya ce a wajen sa annobar da ta aukawa kungiyar sa ta Brazil ta wuce, tuni kuma ya manta da wancan mummunan sakamako da kulaf din kasar ta Brazil ya hadu da shi a gasar da ta gabata.

Guedes ya shaidawa 'yan jarida hakan ne a ranar Asabar, bayan da ya ciwa kulaf din sa na Fluminense kwallaye 2 a wasan da kulaf din ya lallasa Palmeiras 3 da nema.

Guedes dan shekaru 30 da haihuwa ya kasance cikin wadanda ake tsokaci a kan irin rawar da suka taka a waccan gasa da Brazil din ta karbi bakunci, inda aka kammala gasar ya na da kwallo daya tak. Ya kuma bayyana aniyar sa ta daina bugawa kasar Brazil din kwallo bayan da suka sha kashi hannun kungiyar Jamus da ci 7 da 1, a wasan kusa da na karshe da aka buga ran 8 ga watan Yulin da ya gabata.

"Wannan lamari ya riga ya shude, ya yin gasar cin kofin duniya akwai nauyi mai tarin yawa a kai na, kuma ba kamar yadda muka yi fata ba, al'amura basu kasance yadda muka so ba" in ji Guedes, wanda ke jawabi jim kadan bayan tashi daga wasan su na Asabar a filin wasa na Maracana.

Yan zu haka dai Guedes ya jefa kwallaye 7 a raga cikin wasanni 12 da ya bugawa kulaf din sa, a gasar da manyan kulaflikan kasar ta Brazil ke bugawa. Ya kuma yi matukar kokari wajen watsi da dukkanin kallon-hadarin-kaji, da masoya kwallon kafar kasar suka rika nuna masa, bayan rashin nasarar da Brazil din ta kwasa a gasar cin kofin na duniya.

"Farin cikin da 'yan kallo suke nunawa ya yin da na zura kwallaye a raga na karamin karfin gwiwa, abin sha'awa ne taka leda a filin wasan irin wannan dake cike da 'yan kallo, inda da zarar na ci kwallo hakan ke sauya tunani su game da gazawa ta a baya" A ma'anar kalaman Guedes.

Yanzu haka dai nasarar wasannin da kulaf din na Fluminense ya samu ya daga matsayin sa zuwa mataki na 4 a gasar Serie A ta kasar Brazil, da maki 35 cikin wasanni 21. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China