in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar na fatan shiga zamanin internet cikin nasara nan da shekarar 2015
2013-04-08 10:50:22 cri

Kasar Nijar na fatan shiga zamanin internet cikin nasara nan da shekarar 2015, a cewar sakamakon wani taron kara wa juna ilmi kan wannan batu da ya gudana a makon da ya gabata a birnin Niamey tare da taimakon kwamitin kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika UEMOA.

Zaman taron da ya gudana a karkashin jagorancin ministan sadarwa da labarai na kasar Nijar, Salifou Labo Bouche ya hada wakilai kimanin hamsin da suka fito daga hukumomin gwamnatin kasar, bangarorin ma'aikatun sadarwa da kasuwanci, kafofin watsa labarai da kuma kungiyoyin zaman kansu.

A tsawon kwanaki biyu, mahalartan taron sun mai da hankali kan matsalolin da suka shafi shiga zamanin internet a kasashen Afrika dake amfani da harshen Faransanci da kuma kasar Nijar. Manyan batutuwan da aka tattauna sun shafi gudanar da bincike a wannan fanni, fahimtar yadda za'a yi wannan sauyi a kasar Nijar, jadawalin aikin da kuma kalubalolinsa kan kafofin rediyo da kuma ma'aunin sanya hannun kungiyar UEMOA bisa jagorancin wannan babban shiri.

Abin da za'a rike shi ne fita daga aikin gargajiya zuwa zamanin internet nan da shekarar 2015 a kasar Nijar ya zama wajibi, in ji hukumomin kasar Nijar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China