in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kara kai wa yanar gizo ta Internet ta Sin hare-hare daga ketare, musamman ma Amurka
2013-03-10 17:21:26 cri
Hukumar tabbatar da tsaron yanar gizo ta kasar Sin wato CNCERT ta gabatar da sabuwar sanarwa da ke kunshe da kididdigar hare-haren da aka kai wa shafukan yanar gizo ko kuma Internet ta kasar Sin, inda ta ce, hare-haren na tsananta sannu a hankali.

Hukumar CNCERT na ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki a wannan fanni na kare yanar gizon kasar Sin tun daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa ranar 28 ga watan Febrairu a bana. Kuma sakamakon bincikenta ya nuna cewa, a cikin wadannan kwanaki 59 da suka gabata, manyan na'urori masu kwakwalwa fiye da 6747 dake sarrafa saura ta hanyar amfani da manhajoji masu hadari ne suka sarrafa na'urori masu kwakwalwa fiye da miliyan 1 da dubu dari 9 da ke nan kasar Sin, a cikinsu kuma akwai 2194 da ke kasar Amurka wadanda suka sarrafa na'urori masu kwakwalwa miliyan 1 da dubu 287 da ke nan kasar Sin. A dai iya cewa, kasar Amurka ta zama ta farko ta fuskar yawan manyan na'urori masu kwakwalwa da ke sarrafa saura da kuma yawan na'urori masu kwakwalwa da aka sarrafa su a nan kasar Sin.

Yayin da wani jami'in ofishin kula da bayanai kan yanar gizo ta Internet na kasar Sin yake zantawa da manema labaru a kwanan baya, ya nuna cewa, kasar Sin, babbar kasa ce ta fuskar amfani da yanar gizo ta Internet, amma ba ta yi fintikau a fannin ba. Kuma bayanai na hakika masu yawa sun shaida cewa, a shekaru da dama da suka wuce, kasar Sin na daya daga cikin kasashen da suka fi fuskantar hare-haren da ake kai wa yanar gizo ta Internet. Har kullum gwamnatin Sin tana nuna rashin amincewa, da kuma yaki da hare-hare kan yanar gizo ta Internet bisa tanajin dokoki. Haka zalika bisa wannan aniya ta sa kaimi kan tabbatar da tsaro a yanar gizo ta Internet, kasashen Sin da Rasha da sauran kasashe sun gabatar wa Majalisar Dinkin Duniya shirin ka'idojin kasa da kasa game da tabbatar da tsaron bayanai a watan Satumba na shekarar 2011. Sa'an nan kasar Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su tsara ka'idoji kan amfani da yanar gizo ta Internet yadda ya kamata bisa tabbatattun ka'idoji, a kokarin samar da kyakkyawar yanar gizo ta zaman lafiya da tsaro, bisa kuma tsarin hadin gwiwa ba tare da rufa-rufa ba, matakin da kuma zai tabbatar da kiyaye moriyar kasashen duniya baki daya. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China