in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU za ta aiwatar da wani shiri domin rage tsadar internet a Afrika
2014-11-05 14:37:10 cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta bayyana a ranar Litinin cewa, za ta aiwatar da wani shirin da ya shafi samar a ko'ina cikin kungiyarta da hada hadar internet tun daga nahiyar, domin rage tsadar internet. Shirin wannan tsarin Afrika na musanya ta hanyar Internet zai taimaka wajen rage farashin internet, tare da tallafawa shimfida hanyoyin musanyar internet a cikin kasashe da shiyoyin Afrika. Darekta reshen harkokin sadarwa na kwamitin tarayyar Afrika, Christian Minoungou, ya bayyana a yayin wani dandalin shiyya a birnin Nairobi cewa, Afrika na kashe kudi a yanzu haka ga masu kamfanoni daga kasashen waje domin tabbatar da hada hadar internet a nahiyar. Wannan hanya ce ta kashe kudi sosai, kana da rashin inganci sosai wajen kuka da musanyar internet, in ji mista Minoungou a yayin taron kara wa juna sani na AU da shiyyar gabashin Afrika kan tsari da daidaita harkokin internet. Dandalin na kwanaki biyu na da manufar bullo da wani tsarin siyasa na shiyya na tsakanin kasa da kasa domin internet. A shekarar 2010, zaman taron kungiyar AU ya cimma wata sanarwa da ta shafi karfafa dangantakar shiyya domin bunkasa harkokin internet da cigaban yada zangonsu. Ya zuwa yanzu kungiyar AU ta samar da karfin tallafawa nagartattun hanyoyin musanyar internet a cikin kasashe mambobi talatin na kungiyar.

Wannan tallafi ya taimaka wajen saukaka kafa wadatattun hukumomi da horar da injiniyoyin dake kwarewa fasahohin zamani domin kula da harkokin internet da layoyinsu, tare da cibiyoyin musanyar internet, in ji mista Minoungou.

Sakataren zartaswa na kungiyar sadarwar gabashin Afrika (EACO), Hodge Semakula ya bayyana cewa, yanayin fasahohin sadarwa na zamani na TCI ya canja zuwa wani sabon salon cigaban kimiyya da fasaha. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China