in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Amurka sun tattauna batun tsaron yanar gizon Internet
2013-03-15 20:05:37 cri
Ranar Jumma'a 15 ga wata, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a nan Beijing cewa, a daren ranar 14 ga wata, a yayin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa Barack Obama na kasar Amurka suke hira ta wayar tarho, sun yi musayar ra'ayoyi kan batun tsaron yanar gizon Internet, inda mista Xi Jinping ya bayyana matsayin da kasar Sin ta dauka da kuma ka'idojin da take bi, inda ya nuna cewa, yanzu matsalar tsaron yanar gizon Internet tana kara tsananta wanda ta zama wani kalubalen da dukkan kasashen duniya suke mai da hankali a kai ta fuskar tsaro. Kiyaye zaman lafiya da tsaro a yanar gizon Internet inda kuma ake hada kai ba tare da rufa-rufa ba zai dace da moriyar kasashen duniya baki daya, ciki har da kasashen Sin da Amurka. A nata fannin, kasar Sin a tsaye take tsayin daka kan kin amincewa da satar bayanai a yanar gizon Internet, don haka kasar Sin tana son ta rika tuntubar Amurka kan batun tsaron yanar gizon Internet yadda ya kamata. (Tasallah)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China