Daga watan Janairu zuwa watan Mayu na bana, yawan masu amfani da layin intanet ya karu da kashi 52 cikin dari.
Bisa alkaluman da ma'aikatar kula da masana'antu da watsa labarai na zamani ta Sin ta fitar a yau 19 ga wata, an ce, ya zuwa karshen watan Mayun bana, yawan mutanen da suke amfani da wayar salula ya kai biliyan 1.256, a ciki, kashi 60 cikin dari suna amfani ne da wayar salulu wajen shiga intanet.