in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira ga kasashen duniya da su karfafa hadin gwiwa tsakaninsu wajen yaki da ta'addanci
2014-10-09 10:41:17 cri
A jiya Laraba 8 ga wata, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wang Min ya bayyana a birnin New York, hedkwatar MDD cewa, kamata ya yi kasashen duniya su kara hadin gwiwa tsakaninsu domin yaki da ta'addanci bisa sauyawar yanayin da ake ciki.

A wannan rana, kwamiti na shida dake kula da harkokin da ya shafi doka na MDD ya kira taron yaki da ta'addanci, inda Wang Min ya bayyana cewa, yanzu ta'addanci yana samun farfadowakaruwa a duniya baki daya. Bai kamata a yi hakuri a kai baBabu sassauci a kansa. Kamata ya yi kasashen duniya su hada gwiwa su yaki da ta'addanci. Sa'an nan ya kamata a , domin kauracewa nuna bambanci ko ware wasu daga cikinsu, balle ma danganta da su da yin mu'amala da wasu kabilu da addinaial'adu na musamman.

Wang ya ce, kamata ya yi a yaki da ta'addanci bisa manufofi da ka'idojin kundin tsarin mulkin MDD, a girmama ikon mulkin kasa da 'yanci da ikon mallakar cikakken yankin kasa, a kuma bi dokokin duniya a fannin amfani da makamai.

Bayan haka, Wang ya kara da cewa, kungiyar ta'addanci ta Sherqiy Türkistan tana kawo babbar barazana ga kasar Sin a yanzu. Gwamnatin Sin tana dora matukar muhimmanci kan hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashen duniya wajen yaki da ta'addanci, kuma tana kokarin sa kaimi ga wannan aiki. Ya ce, Gwamnatin gwamnatin Sin tana goyon baya ga kokarin sauran kasashe a fannin yaki da ta'addanci, ta ba da kayayyakin agaji da horaswa da makamantansu ga sauran kasashe masu tasowa bisa iyakacin kokarinta.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China