141117-kasar-sin-ta-kara-tura-wasu-likitoci-don-tallafawa-kokarin-dakile-ebola-bello.m4a
|
Tawagogin 4 da suka tashi a daren ranar 14 ga wata sun kunshi ma'aikatan lafiya 163 da suka zo daga jami'ar koyon fasahar likitanci ta rundunar soja ta 3 ta kasar Sin, gami da wani bangare na sojojin Shen'yang,wadanda za su yi aiki a cibiyar jinyar wadanda suka kamu da cutar Ebola mai gadaje 100 da kasar Sin ta kafa a kasar Laberiya. Sa'an nan tawaga ta 2 ta kunshi kwararru masu binciken alamun kamuwa da cutar Ebola fiye da 40, wadanda za su maye gurbin rukuni na farko na kwararrun kasar Sin dake kasar Saliyo, inda za su gudanar da aikin binciken kwayoyin cutar Ebola da jinyar wadanda suka kamu da cutar a wani asibitin da kasar Sin ta gina wa Saliyo. Ban da su kuma akwai kuma tawaga ta 3 da babban kwamishina mai kula da aikin tallafawa kasashen Afirka ta fuskar kau da annobar, mista Xu Shuqiang, ya jagoranta, wadda za ta mayar da hankali kan aikin dakile cutar Ebola a yammacin Afirka, tare da jagorar masu aikin jinya dake wajen. A karshe sai tawaga ta 4 da ta kunshi mutum daya kawai, wato Feng Zijian, mataimakin darektan cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasar Sin, wanda zai taka rawa a matsayin mai ba da shawara ga shugaban tawagar MDD mai kula da shirin yaki da cutar Ebola, wajen koyarwa gamayyar kasa da kasa fasahar da kasar Sin ta samu a lokacin da ta magance yaduwar cutar SARS.
Ya zuwa yanzu yawan likitoci da masanan da kasar Sin ta tura zuwa kasashen yammacin Afirka dake fama da radadin annobar Ebola ya haura 300. Haka zalika a cewar Teng Guangsheng, wani jami'i mai kula da aikin hana yaduwar cutar Ebola, an kusan kammala aikin gina cibiyar yakar cutar Ebola a kasar Laberiya.
"Sojojin kasar Sin PLA suna kokarin taimakawa Laberiya wajen tinkarar cutar Ebola. Tawagar ma'aikatan lafiya da ta tashi a wannan karo ta kunshi mutane 163, ciki har da kwararru masana 22.
Kuma bayan da suka isa Laberiya, za su fara aikinsu a cibiyar tinkarar Ebola da muke taimakawa wajen gina ta. Ana sa ran bude cibiyar kafin ranar 25 ga watan Nuwamba, inda za a sanya gadaje 100."
A nasa bangaren, Du Ning, likita a asibitin rundunar soja ta 302 ta kasar Sin, wanda kuma yana cikin tawagar zuwa kasar Saliyo, ya ce likitocin kasar Sin za su taimakawa jama'ar yammacin Afirka, da tallafawa kokarin da ake na jinyar masu dauke da kwayoyin cutar Ebola.
"Al'ummar wurin na fama da talauci, kana suna fuskantar matsala a fannin samun jinya. Don haka jama'ar wurin na cikin wani hali na rashin tabbas. Shi ya sa yadda muke taimaka musu wajen samun jinya zai sanya su samun kwanciyar hankali. Sa'an nan yadda aka hada fasahar gargajiya ta kasar Sin da fasahar zamani wajen jinyar masu dauke da cutar Ebola zai samar da wata sabuwar dama a kokarin tinkarar cutar, wannan shi ne burin da ke cikin zuciya ta."
A nasa bangare kuma, Dudley Thomas, jakadan kasar Laberiya dake kasar Sin, ya yaba wa kasar Sin kan yadda take kokarin tallafawa Laberiya wajen dakile cutar Ebola, ya ce,
"Sanin kowa ne ana samun yaduwar cutar Ebola a Laberiya, Saliyo da Guinea. Don magance wannan matsala kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa, kuma ta shiga wannan aiki nan da nan. Da farko dai, sun tura mana likitoci tare da ba mu tallafin kayayyaki, sa'an nan sun sake tura wa kasar Laberiya wata babbar tawaga, wannan yana da muhimmanci sosai. A ganina wadannan likitoci jarumai ne, saboda sun zo kasarmu don taimakawa jama'armu, ta yadda za su kubuta daga wannan cuta ta Ebola."
Ana ganin cewa, zuwa karshen watan Nuwanban da muke ciki, yawan likitocin kasar Sin dake yankunan da ke fama da cutar Ebola zai kai kimanin 400. Kana idan aka duba jimmillar mutanen, ya zuwa yanzu kasar Sin ta tura likitoci da kwararru kimanin 1000 zuwa kasashen yammacin Afirka 3 da suke fama da cutar ta Ebola.(Bello Wang)