A ran 16 ga wata, an rufe taron koli na shugabannin kungiyar G20 wanda aka shafe kwanaki 2 ana yinsa a birnin Brisbane na kasar Australia. A yayin bikin rufe taron, an fitar da "Hadaddiyar Takarda", kuma an zartas da "shirin aiki na Brisbane", har ma an fitar da matakai fiye da dubu 1 na bunkasa tattalin arzikin duniya, samar da karin guraban aikin yi da yin kokarin yin cinikayya cikin 'yanci.
Za a shirya taron koli na G20 na shekara mai zuwa a kasar Turkiya, kuma za a shirya na shekarar 2016 a nan kasar Sin. (Sanusi Chen)