Maganar kyautata aikin kamfanonin gwamnati ta kasance wani muhimmin kalubale da ya kamata a warware a tsawon wannan sabuwar shekara. Matakin kuma shi ne na kawo gwargwadon gyara ga kamfanonin gwamnati ta yadda za su taimakawa kasafin kudin kasa da ci gaban kasa baki daya, in ji wannan sanarwa.
Bisa wannan mataki, in ji sanarwar, ta tuni aka tura wata tawagar yin kididdiga domin kimanta kadarorin kamfanonin gwamnatin guda takwas da suka hada kamfanin sadarwa na Benin Telecom, tashar ruwa na Port Autonome na Cotonou, kamfanin wutar lantarki da ruwa kasar Benin (SBEE), kamfanin kasa na bunkasa noma (SONAPRA), kamfanin kasuwancin kayayyakin man fetur na SONACOP, kamfanin bunkasa noman auduga (SODECO), kafar gidan rediyo da talabajin na kasar Benin (ORTB), asusun kariyar jama'a (CNSS) da kuma kamfanin kayayyakin tashoshin ruwa na kasar Benin (SODECO). (Maman Ada)