Kundin wannan tsarin shiri an rattaba hannu kansa a ranar Alhamis a birnin Cotonou tsakanin ministan cigaba da nazarin tattalin arzikin kasar Benin, mista Marcel de Souza da jami'ar dake kula ayyukan MDD a kasar Benin, Nardos Bekele-Thomas.
Wannan tsarin shiri zai taimaka wa cibiyoyin MDD wajen tallafawa gwamnatin kasar Benin da sauran masu ruwa da tsaki da ma kungiyoyi na kasar domin cimma maradun sabon karni na cigaba da na jadawalin shiga shekarar 2015. A cikin wannan tsarin shiri, mun dauki niyyar shigar da taimakonmu cikin shekaru biyar masu zuwa bisa tsarin cimma muhimman batutuwa na cigaban kasa kamar yadda aka tabbatar da su a cikin manyan hanyoyi takwas na muradun sabon karni na cigaba, in ji madam Bekele-Thomas.
Bugu da kari, wannan tsarin shiri zai fi maida hankali kan muhimman fannonin cigaba na kasar Benin da suka rataya kan batutuwa shida na cigaba masu muhimmanci kan samar da guraban aikin yi ga matasa da mata, rigakafi da daukar nauyin masu fama da ciwon sida, lafiyar uwa da danta, karfafa tsarin samar da bayanai na kididdiga na kasar da kuma rigakafi da daidaita bala'u daga indallahi. (Maman Ada)