in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Benin ya gana da Shugaban kasar Gambiya dangane da rikicin Guinea Bissau da Mali
2012-08-23 21:06:49 cri
Ministan harkokin wajen kasar Benin Bako Arifari Nassiro yana kasar Gambiya inda ya gana da Shugaban kasar Yahya Jammeh dangane da halin da ake cikin yanzu kan rikicin siyasa a kasar Guinea Bissau da kuma Mali.

Ministan wanda ya isa Banjul babban birnin kasar Gambiya a jiya laraba 22 ga wata ya gana da Shugaba Yahya Jammeh a wannan rana a matsayin sa na manzo na musamman na Shugaban kasar Benin Yayi Boni wanda shine shugaban kungiyar tarayyar kungiyar kasashen Afrika AU.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar,Arifari Nassiro yace ya nemi shawarwari ne daga wajen Shugaba Yahya Jammeh game da yadda za'a kawo karshen matsalar da ake fuskanta a wadannan kasashe biyu na Afrika.

A tabakin sa " dukkan mu 'yan kasashen nahiyar afrika na yamma ne kuma mambobin kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU, sannan kuma Shugaba Jammeh yana da kwarewa wajen wanzar da zaman lafiya da daidaito a kasar sa da ma yankin nahiyar baki daya. ''

Nassiro ya bayyana cewa kungiyar AU ta na nuna damuwa matuka game da halin da ake ciki a kasar Mali da Guinea Bissau wadanda suka fuskanci juyin mulkin soja a watan maris da afrilun bana ko wannen su.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China