A gun taro na kwanaki biyu, shugabanni kasashen sun tattauna halin tattalin arzikin duniya, tsarin hada-hadar kudi na duniya, samun ci gaba, ciniki, samun aikin yi da dai sauransu. Bayan taron sun fitar da sanarwar hadin gwiwa. A gun taron manema labaru bayan taron, firaministan kasar Ingila David Cameron ya bayyana cewa, an samu nasara a gun taron koli na kungiyar G20 a wannan karo. Ya ce, "A ganina, an samu nasara a wannan taro, wanda ya taimaka wajen magance gamuwa da wasu matsaloli yayin da ake inganta tattalin arzikin duniya. Wannan ne karo na farko da wasu manyan kasashen duniya suka tattauna wadannan matsaloli tare, da kuma yadda za a warware su."
Haka kuma firaminista Cameron ya bayyana cewa, a gun taron kolin, an tattauna yadda za a tsara sabbin ka'idojin hada-hadar kudi da yin kwaskwarima kan tsarin bankuna, kuma an samu ci gaba wajen warware matsalar rashin daidaito kan tattalin arzikin duniya da kuma matsalolin da ake fuskanta a yanki mai amfani da kudin Euro. Ban da wannan kuma, Cameron ya nuna godiya ga kasar Sin musamman domin muhimmiyar rawa da ta taka a gun taron. Ya ce, "Muna maraba da alkawarin musamman da kasar Sin ta bayar, wato sa kasuwa ta kara yin tasiri ga canjin darajar kudin Sin Renminbi."
A gun taron manema labaru, shugabar asusun bada lamuni na duniya wato IMF Christine Lagarde ta bayyana cewa, kasashe 37 sun yi alkawarin kara zuba jari ga IMF don kara azama ga IMF da ta taimaka wa kasashe 188 membobin asusun da su farfado da tattalin arzikinsu. Kana ta nuna godiya ta musamman ga kasar Sin. Ta ce, "Ina nuna godiya sosai ga kasar Sin domin kara zuba jari ga asusun IMF da ta yi. Ni da shugaban kasar Sin Hu Jintao mun yi shawarwari, inda ya jaddada niyyar kasar Sin wajen kara taka muhimmiyar rawa a yayin da hadin gwiwarta da asusun IMF. A ganinmu, tilas ne a gaggauta yin kwaskwarima kan asusun IMF."
Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, kungiyar EU muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa ta kasar Amurka ce. Rikicin bashi dake addabar kasashen Turai ya kawo illa ga kasar Amurka, sabo da haka, kasar Amurka tana fatan nahiyar Turai za ta warware rikicin cikin hanzari.
Game da batun kara azama ga samun ci gaba da samar da aikin yi da aka tattauna a gun taron kolin, Obama ya ce, "A matsayin kasa mafi girma a fannin tattalin arziki a duniya, kasar Amurka tana kokari wajen sa kaimi ga samar da aikin yi da samun ci gaba. Amma idan aka yi la'akari da dogon lokaci, za ta ci gaba da yin kokarin mayar da ayyukan hukumomin kudi a kasar." (Zainab)