A gun bikin, shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma, ya bayyana cewa, mutum-mutumin yana alamta Nelson Mandela na rungume da kasar Afrika ta Kudu, da al'ummar ta, wanda ya nuna cewa jama'ar kasar Afrika ta Kudu suna da hadin kai game da bin turbar demokuradiyya.
Shi ma a nasa tsokaci don gane da hakan, ministan kula da harkokin fasahohi da al'adun kasar Mashati Lai cewa ya yi, dalilin da ya sa aka kafa mutum-mutumin Nelson Mandela shi ne, tunawa da kokarin da ya yi a duk rayuwarsa wajen samar da 'yanci, da neman sulhuntawa tsakanin kabilun kasar daban daban.
An ce tsayin mutum-mutumin na Mandela ya kai kimanin mitoci 9, an kuma kafa shi ne a wani dandamalin dake gaban fadar shugaban kasar.(Bako)