A yayin ganawarsu a wannan rana, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin na mai da hankali sosai kan ziyarar aikin da shugaban kasar Amurka Barack Obama zai kawo a kasar Sin da kuma sa ran da ake yi zai halarci kwarya-kwaryan taron shugabannin kungiyar APEC. Ana fatan kasashen biyu za su iya dukufa tare don cimma nasarar ziyarar aikin da shugaba Obama zai gudanar a kasar Sin, da kuma ganawar shugabannin biyu, ta yadda za a iya kyautata dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.
A nasa bangaren kuma, John Kerry ya bayyana cewa, goyon bayan da kasar Sin da kuma kasar Amurka suke baiwa juna, musamman kan manyan harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya ya dace matuka da moriyar kasashen biyu. Mr. Obama na sa rai sosai kan ziyarar aikin da zai kai a kasar Sin, kuma kasar Amurka na muradin hadin gwiwa da kasar Sin domin samun kyakkyawan sakamako dangane da ziyarar aikin shugaba Obama a kasar Sin, da kuma bunkasa sabuwar dangantakar manyan kasashen Sin da Amurka . (Maryam)