in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron ministocin APEC
2014-11-07 20:30:34 cri
Yau Jumm'a 7 ga wata aka bude taron ministocin kungiyar APEC ta hadin kan tattalin arzikin Asiya da tekun Pasific a nan birnin Beijing. Ministocin harkokin waje da na kasuwanci na kasar Sin sun halarci taron tare da gabatar da jawabin bude taron a matsayin shugabannin taron.

Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, cikin shekaru 25 da kafuwar kungiyar APEC, kungiyar ta ba da babbar gudummawa wajen bunkasa tattalin arzikin Asiya da tekun Pasifik tare da kyautata zaman rayuwar al'ummar shiyyar. Akwai manyan sauye-sauye ga dangantakar da ke tsakanin Asiya-Pasifik da sauran sassan duniya. Kasashen duniya na bukatar shiyyar Asiya –Pasifik ta kasance har kullum cikin jituwa da ci-gaba da kuma albarka.

Gao Hucheng, ministan kasuwanci na kasar Sin a nasa bangaren ya ce, yanzu haka, yawan cinikin da mambobin kungiyar ta APEC ke yi da kasashen waje ya kai kashi 48% na duniya baki daya a yayin da jimillar tattalin arzikin kasashen ta kai kashi 57%, abin da ya shaida muhimmiyar rawar da shiyyar ke takawa a fannin tattalin arzikin duniya, da kuma shiyyar da take sa kaimi wajen karuwar tattalin arzikin duniya. A sabon yanayin da ake ciki, ya kamata mambobin kungiyar su nuna basira da kuzari, a kokarin kiyaye tsarin ciniki na tsakanin bangarori da dama da kuma gaggauta dunkulewar shiyyar baki daya. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China