in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Palesdinu da Isra'ila sun daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta cikin dogon lokaci
2014-08-27 10:33:13 cri

A ranar talata 26 ga wata, Palesdinu da Isra'ila suka daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta cikin dogon lokaci sakamakon shiga tsakani da Masar da sauran bangarorin da abin ya shafa suka yi. A dangane da hakan MDD ta yi maraba da wannan sakamako tare da yin kira ga bangarorin biyu da su maido da shawarwarin siyasa ba tare da bata lokaci ba.

An fara aiwatar da wannan yarjejeniya a zirin Gaza da misalin karfe 7 na daren wannan ranar ta Talatan bisa agogon wurin. Dimbin Jama'a sun fita kan tituna, suna daga yatsunsu nuna alamun nasara, tare da sauran hanyoyin da suke bi domin bayyana farin cikinsu kan kawo karshen rikici wanda aka shafe kwanaki 50 ana yinsa.

A wannan ranar kuma, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya bayar da wata sanarwa, inda ya yi maraba ga Palesdinu da Isra'ila da suka sanar da tsagaita bude wuta a zirin Gaza ba tare da kayyade wa'adi ba. Sanarwar ta ce, idan ana son samun wata kyakkyawar dama ga zirin Gaza da Isra'ila, to, ya kamata a tsagaita bude wuta cikin dogon lokaci. Mr. Ban ya ce ya kamata bangarori daban daban su sauke nauyin da ke bisa wuyansu. Sanarwar ta ci gaba da cewa, idan ba a warware ainihin tushe na rikicin Palesdinu da Isra'ila ba, kokarin da ake yi wajen shimfida zaman lafiya zai iya zama wani dalilin da zai tunzura tashin hankali a nan gaba. Dole ne a bar harkokin zirin Gaza a karkashin kulawar halaliyar gwamnatin kasar Palesdinu, tilas ne a kawar da kangiya da ake yi wa zirin Gaza, kana tilas ne a ba da zaman lafiya ga Isra'ila. Mr Ban ya bayyana fatan cewa yarjejeniyar za ta iya bude yunkurin siyasa, domin shimfida zaman lafiya cikin dogon lokaci a tsakaninsu. Shugaban na MDD daga nan sai ya yi kira ga bangarorin biyu da su sake zama a kan teburin shawarwari, domin daddale yarjejeniyoyin kan matsayin su na karshe. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China