Sanarwar ta bayyana cewa, kwamitin sulhu ya kalubalanci sojojin tsaron kasar Burkina Faso da su mika iko ga gwamnatin rikon kwarya dake karkashin jagorancin fararen hula, da kuma daukar matakai domin maido da odar tsarin mulkin kasar ba tare da bata lokaci ba. Kwamitin sulhu ya yi kira ga bangarori daban daban dake kasar da su yi kokari wajen samun zaman lafiya da demokuradiyya, da gudanar da zabe bisa tsarin mulkin kasar cikin 'yanci, da adalci, da kawar da bambance-bambance. (Zainab)