Dubban masu boren dai sun bayyana Kouame Lougue, tsohon janar a rundunar sojin kasar, kuma tsohon ministan tsaro a matsayin wanda ya fi dacewa ya jagoranci rikon kwaryar, bayan murabus din shugaba Blaise Compaore.
Masu boren dai na kallon Nabere Traore a matsayin daya daga wadanda aka dama da su a rusasshiyar gwamnatin shugaba Compaore, don haka kasancewar sa jagoran gwamnatin rikon kwaryar kasar a yanzu, tamkar komawa gidan jiya ne.