An dai buga wannan wasa ne a daren ranar Asabar a filin wasa na Blida. Kuma kulaf din na ES Setif ya cimma nasara ne da tsiran maki, bayan tashi kunnen doki 2 da 2 a gidan Vita, yayin wasan zagayen farko da aka buga cikin makon da ya gabata.
Wannan ne dai karo na farko da wani kulaf din kasar Aljeriya ya lashe kofin zakarun nahiyar da aka sauyawa suna, a baya cikin shekarar 1987 kulaf din na ES Setif ya taba lashe kofin kulaflikan Afirka da aka yiwa lakabi da "Cup of Champions Clubs"
Yanzu haka dai kulaf din na ES Setif zai karbi kyautar kudi har dalar Amurka miliyan 1 da rabi, zai kuma wakilci nahiyar Afirka, a gasar kulaflikan duniya da hukumar FIFA ke shiryawa, wanda zai gudana a wata mai zuwa a kasar Morocco.