in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kosgei daga Kenya ya lashe gasar gudun yada-kanin wani ta birnin Nairobi
2014-10-31 10:12:09 cri
Dan wasan tseren kasar Kenya Peter Kosgei, ya samu nasarar lashe gasar tseren yada-kanin wani karo na 12 da aka kammala ranar Lahadin data gabata a birnin Nairobin kasar Kenya. Gasar da bankin Standard Chartered ke daukar nauyin shiryawa a duk shekara.

Kosgei dan shekaru 26 da haihuwa ya kammala gudun sa cikin awa 2 da mintuna 12 da dakika 24.

Dan wasan tseren wanda ya bayyanawa manema labaru cewa ba shi da wani manaja, bai kuma taba samun nasara a wata babbar gasa a baya ba, ya ce yana fatan wannan nasara da ya samu za ta share masa fagen cimma wasu karin nasarorin a nan gaba.

Kosgei dai ya yiwa ragowar 'yan wasan rata ne tun daga mita 200 gabanin kaiwa karshen tseren, wanda hakan ya bashi nasarar lashe tseren tare da samun kyautar kudi har dalar Amurka 18,000.

Sauran 'yan wasan dake biye da Kosgei sun hada da Elisha Barno wanda ya zamo na biyu, ya kuma kammala na sa gudun cin sa'a 2 da mintuna 12 da dakika 28, ya yin da shi kuma Kirui Weldon ya kasance a matsayi na Uku.

A ajin mata kuwa, Eunice Jeptoo ce ke kan gaba, inda ta lashe gasar tseren yada-kanin wanin cikin sa'a 2 da mintuna 43 da dakika 2, sai kuma Hyline Kwambai a matsayi na biyu, wadda ta kammala gudun ta cikin sa'aoi 2 da mintuna 44 da dakika 15. Sai kuma Janet Jeruto ta Uku wadda ta kammala gudun ta cikin sa'oi 2 da mintuna 44 da dakika 31.

Cikin 'yan wasan gudun da suka bayyana a wannan gasa ta birnin Nairobi dai hadda Dennis Kimetto, wanda ya taba lashe makamanciyar wannan gasa ta duniya, da kuma Geoffrey Mutai, mai rike da kanbin lamba uku a jerin 'yan wasa mafiya gudu a gasar gudun na yada kanin wani. Sai kuma Irene Jerotich wadda ta lashe gasar gudun yada-kanin wani ta kasashe renon Ingila da aka kammala 'yan makwannin baya.

'Yan tsere sama da 17,000 ne dai suka halarci wannan gasa ta kilomita 10, ciki hadda na ajin guragu dake kan keke ajin mata da maza.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China