in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Japan da Koriya ta Kudu za su fafata a gasar wasannin nahiyar Asiya da ke tafe a birnin Incheon
2014-09-19 10:19:33 cri
Tawagar 'yan wasan kasar Sin ta halarci wasannin nahiyar Asiya a karon farko a shekarar 1974, inda kasar ta Sin, da Japan da Koriya ta Kudu suka samu matsayi na uku a sahun jerin kasashen da suka samu lambobin yabo a wasanni 10 da suka shiga.

Wadannan kasashe uku su ne mafiya karfi tsakanin sauran kasashen Asiya, don haka ake hasashen mai yiwuwa ne su ci gaba da zama a matsayin su na ukun gaba a gasar wasannin na wannan karo, wanda za a gudanar a birnin Incheon na kasar Koriya ta Kudu. A ya yin wasannin dake tafe, kasashen uku za su yi takarar neman nasara a wasanni daban daban.

A matsayin gasar na daya daga manyan gasanni mafiya girma, a wannan karo za a lashe lambobin zinari 38 a wasan iyo. Kuma fafatawar da za a yi tsakanin Sun Yang na kasar Sin da Pak Tae-hwan na kasar Koriya ta Kudu na cikin takara mafi jawo hankalin masu sha'awar wasan iyo a gasar ta wannan karo ajin linkaya mai 'yanci.

Shi dai Pak Tae-hwan ya cimma nasarori a gasar wasan iyo ta kasarsa ta Koriya ta Kudu, da kuma gasar wasan iyo ta Pan-Pasific a shekarar bana, ya yin da Sun Yang na Sin ke ganin rashin halartar sa gasar Pan-Pasific ce ta baiwa Pak Tae-hwan nasarar da ya samu, wato dai a ganin sa zai iya doke Pak da ya samu halartar gasar ta Pan-Pasific.

Sun Yang da Pak Tae-hwan za su yi takarar neman lambar yawo a dakin wasan iyo mai suna Pak Tae-hwan. Ga Sun Yang, wannann wasa yana da babbar ma'ana ga nasarar sa, musamman ganin za a yi wasan ne a dakin linkaya mai sunan dan takarar da zai kara da shi.

Ban da takara tsakanin Sun Yang da Pak Tae, wasa tsakanin 'yan wasan iyo na kasar Sin da na kasar Japan, su ma za su yi matukar jawo hankalin masu sha'awar wasan iyo.

Game da wasan guje-guje da tsalle-tsalle, akwai lambobin zinari 47 da za a ci a gasar wasannin ta Asiya a wannan karo. A wasan gudun mita dari na maza, mashahurin dan wasa daga kasar Japan Kiryuu Yoshihide ya kamata ya kasance cikin 'yan takara tare da 'yan wasa na kasar Sin Zhang Peimeng, da Su Bingtian, sai dai ya samu rauni wanda hakan ya sanya shi bakin ciki tare da wajabta masa janyewa daga gasar a wannan karo.

Ko da yake ba za a ga Kiryuu Yoshihide a gasar ba, duk da haka 'yan wasan kasar Sin da na Japan suna da kwarewa wajen takara da cimma nasara a wasannin da za a yi.

A wasan kwallon kwando, kungiyar kasar Sin ta mata da ta Japan da ta Koriya ta Kudu suna rukuni daya. Kuma idan tawagar Sin tana da burin samun kyakkyawan sakamako, akwai bukatar ta doke Japan da Koriya ta Kudu.

Kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin za ta fafata da takwarar ta ta Japan a rukuni daya. Game da hakan kocin tawagar Sin Hao Wei ya bayyana cewa, kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta Japan ta na da karfi fiye da sauran kulaflikan nahiyar Asiya, da ma na sauran sassan duniya. Amma kulaf din kasar Sin ya na da karfi da kwarewa da zai bata damar iya doke Japan, don haka burin kungiyar wasan kwallon kafar mata ta kasar Sin a wannan karo shi ne doke kungiyar Japan. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China