Magatakardan MDD Ban Ki-moon ya yi kakkausar suka a kan yadda ake gitta wasu sharuda da nuna banbanci ga ma'aikata kiwon lafiya wadanda ke sadaukar da rayuwarsu domin yaki da cutar Ebola mai saurin kisan bil-adama.
Ban Ki-moon wanda ya yi wannan jawabin a yayin wani taron manema labarai a babban birnin kasar Austria ya ce, bai kamata ba ma'aikata lafiya wadanda ke taimakawa majiyyata da suka kamu da cutar Ebola, a hana su gudanar da ayyukansu saboda mahimmancin ayyukan nasu, musamman idan aka yi la'akari da cewar, su kansu ma'aikatan kiwon lafiya na cikin barazana ta kamuwa da cutar.
Ban ya ce, fiye da ma'aikatan lafiya 250 ne suka rasu a yayin da suke gudanar da ayyukansu na kulawa da majiyyata wadanda suka kamu da cutar Ebola mai saurin kisan bil'adama. (Suwaiba)