in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saliyo ta jinjinawa Sin bisa tallafin kayan yaki da cutar Ebola
2014-11-04 10:33:38 cri

Ofishin wakiliyar din din din ta kasar Saliyo a MDD Yvette Stevens, ya aikewa takwaransa na kasar Sin wani rubutaccen sako, dake bayyana godiyar game da gudummawar kayan tallafin yaki da cutar Ebola da Sin ta baiwa Saliyon.

Cikin wasikar, Yvette Stevens ta ce, Saliyo na fatan ci gaba da hadin gwiwa da mahukuntan kasar Sin, a kokarinta na kawo karshen yaduwar cutar ta Ebola.

Tun dai barkewar wannan annoba a watan Fabarairu, kasar Sin ta zamo ja gaba a jerin kasashen da ke samar da taimakon kayan aiki, da na kwararru bisa bukatar da hukumar lafiya ta duniya WHO ta gabatar.

Baya ga tallafin kudade, da abinci da kayan kariyar yaduwar cutar, kasar ta Sin ta kuma kafa wasu dakunan gwaji, da wuraren kebe masu dauke da cutar, ta kuma tura tawagar kwararru, da likitocin kasashen da cutar ta fi kamari.

Ya zuwa yanzu kasar ta Sin ta samar da tallafin da ya kai na dalar Amurka miliyan 122 ga kasashen yammacin Afirka, inda cutar ta fi kamari.

A daya hannu kuma hukumar WHO ta ce, ya zuwa 29 ga watan Oktobar ya da gabata, mutane 13,567 ne aka hakikance sun kamu da cutar, baya ga mutane 4,951 da tuni suka rasa rayukansu sakamakon cutar ta Ebola. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China