A yau Litinin 3 ga wata, a nan Beijing ne, Fang Aiqing, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin ya sanar da cewa,daga watan Afrilu zuwa na Satumban bana, gwamnatin Sin ta tsara matakan ba da tallafin yaki da Ebola har sau 3, inda ta bai wa kasashe 13 na Afirka kayayyakin ba da kariya da yaki da cutar Ebola, abinci da kudade, ta kuma aika da masanan ilmin kiwon lafiyar al'umma da ma'aikatan lafiya, tare da gina dakunan gwaje-gwaje, sa'an nan ta bai wa hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO da kungiyar tarayyar Afirka wato AU da sauran kungiyoyin shiyya-shiyya da na kasa da kasa kudin taimako. Ya zuwa yanzu kasar Sin ta kammala zagaye na 3 na ba da kayayyakin agajin.
A wannan rana, ofishin yada labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya taron manema labaru dangane da yadda kasar Sin take ba da taimako wajen yaki da cutar ta Ebola da yin rigakafin cutar.
A yayin taron, mista Fang ya kara da cewa, baya ga ba da taimako a tsakanin bangarori 2, kasar Sin tana mara wa MDD da WHO da sauran kungiyoyin kasa da kasa baya wajen yaki da cutar. Kasar Sin za ta hada kai da kasashen duniya ciki had da kasashen da ke fama da cutar da jama'arsu wajen yaki da cutar yadda ya kamata a karkashin shugabancin MDD da WHO.(Tasallah)