in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram a kalla 100
2014-09-13 16:12:12 cri
A kalla mayakan kungiyar Boko Haram 100 aka kashe a ranar Jumma'a a wani samamen rundunar sojojin Najeriya ta kai a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, in ji ministan tsaro. Haka kuma wasu da dama sun raunana sosai a yayin da sojojin Najeriya suka hada karfinsu tsakanin sojojin kasa da na sama domin kai babban samame kan wasu mayakan Boko Haran kusan dari biyu a yayin da suka yi wani yunkurin kwace ikon garin Konduga, mai tazarar kilomita 40 da Maiduguri, hedkwatar jihar Bormo mai fama da tashin hankali a arewacin kasar, in ji ma'aikatar tsaron Najeriya a cikin wata gajeriyar sanarwa.

Yawancin maharan da aka kashe sun sha lugudan wuta har ma ba'a iya gane su bayan an kwace kusan sa'o'i ana gumurzu bisa jaruntakar sojojinmu, in ji wani babban jami'in sojan Najeriya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China