Bisa sakamakon da hukumar zaben kasar Mozambique ta gabatar a birnin Maputo a wannan rana, an ce, dan takara na jam'iyyar Renamo, Afonso Dhlakama ya samu kuri'u na kashi 36.61 cikin dari, kuma dan takara na jam'iyyar MDM, Daviz Simango ya samu kuri'u na kashi 6.36 cikin dari.
Haka kuma cikin kujeru 250 na majalisar dokokin kasar, jam'iyyar Frelimo ta samu kujeru 144, adadin da ya ragu da 47 bisa na majalisar da ta gabata. Yawan kujerun da jam'iyyar Renamo ta samu a majalisar dokokin kasar a wannan karo ya karu da 38 inda ya kai 89. Kuma yawan kujerun mallakar jam'iyyar MDM ya karu daga 8 zuwa 17.
Kafin a gabatar da sakamakon zaben, shugaban hukumar zaben kasar Abdul Carimo ya bayyana wasu ayyukan da suka sabawa ka'idojin zaben, kuma ya ce ana yin bincike kansu
Bayan da aka gabatar da sakamakon kwarya-kwarya a ranar 18 ga wata, jagoran jam'iyyar Renamo Dhlakama yayi zargin cewa an tabuka magudi yayin zabe, tare da yin watsi da sakamakon zaben. Sai dai jam'iyyar Frelimo ta ki amince da zargin jam'iyyar Renamo.(Zainab)