in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi maraba da kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta a tsakanin bangarorin biyu da ke rikici a Mozambique
2014-09-12 20:18:16 cri
Kwanan baya, gwamnatin kasar Mozambique da kungiyar dake adawa da gwamnati suka kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta don kawo karshen rikicin dake tsakaninsu.

Dangane da lamarin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yau Jumma'a 12 ga wata cewa, kasar Sin tana maraba da kulla wannan yarjejeniyar, kuma ta nuna yabo ga bangarorin biyu dangane da kokarinsu na shimfida zaman lafiya a kasar da kuma neman sulhunta jama'ar kasar. A matsayinta aminiyar kasar Mozambique, kasar Sin tana fatan bangarorin da abin ya shafa na kasar Mozambique za su ci gaba da dukufa don samun dauwamammen zaman lafiya da bunkasuwar kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China