Baya ga wakilan tsagin biyu, an kuma gayyaci wasu 'yan kallo daga fannin ayyukan soja na kasashen waje, domin taimakawa mayakan jam'iyyar Rename a aikin kawar da makamai, da shigar da su cikin rundunar sojojin tsaron kasar.
Game da yarjejeniyar da aka kulla, shugaban tawagar wakilan jam'iyyar ta Renamo ya ce, dakarun jam'iyyarsa, za su dakatar da daukar dukkanin wani mataki na nuna kiyyaya ga gwamnatin kasar. Ya ce yarjejeniyar tsagaita bude wutar da suka shiga da gwamnatin kasar ta shaida matakin da Mozambique ta dauka, na bude sabon shafin samun bunkasuwa, wanda ke wakiltar kyakkyawan fatan jama'ar kasar. (Zainab)