in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude tashoshin jefa kuri'a a kasar Mozambique
2014-10-15 15:32:01 cri
A yau Laraba ne al'ummar kasar Mozambique sun je tashoshin jefa kuri'ar zabe domin zaben shugaban kasarsu na 4 tun bayan da kasar ta samu 'yancin kanta a shekarar 1975. Haka zalika kuma, za su jefa kuri'u don zaben sabbin 'yan majalissun dokoki da na larduna daban daban.

A zaben shugaban kasar za a kara ne a tsakanin tsohon ministan tsaron kasar, Filipe Nyusi, dan takarar jam'iyyar Frelimo dake rike da ragamar mulki, da Afonso Dhlakama, shugaban jam'iyyar adawa ta Renamo, gami da Daviz Simango, shugaban jam'iyyar adawa mafi girma ta 2 ta MDM. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China