in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakaru masu adawa da gwamnatin kasar Mozambique sun kara kai hare-hare a kasar
2014-07-22 10:06:10 cri
Bangaren 'yan sandan jihar Sofala dake tsakiyar kasar Mozambique ya bayyana a ranar 21 ga wata cewa, yawan hare-haren da jam'iyyar adawa ta RENAMO ta kai a kasar a watan Yuni ya karu, wadanda suka haddasa mutuwar fararen hula 6.

Bangaren 'yan sandan ya bayyanawa 'yan jarida cewa, bisa kididdigar da aka yi, an ce, jam'iyyar RENAMO ta kai hare-hare sau 29 a watan Yuni, yawancinsu an kai su ne a kan motoci dake kan hanyoyin dake a tsakanin arewaci da kudancin kasar. Hare-haren da jam'iyyar ta kai sun haddasa mutuwar fararen hula 6, kuma 21 daga cikinsu sun ji rauni mai tsanani. Yawan mutane da suka mutu ko suka ji rauni a watan Yuni a sakamakon hare-haren ya karu sosai bisa na watan Mayu.

Ban da wannan kuma, an ci gaba da yin shawarwari a tsakanin wakilan gwamnatin kasar Mozambique da na jam'iyyar RENAMO, amma har yanzu bangarorin biyu ba su cimma daidaito kan tsagaita bude wuta a tsakaninsu da shigar da dakarun jam'iyyar zuwa sojojin kasar ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China