Wannan ne dai karo na 13 da kungiyar ta samu irin wannan nasara cikin shekaru 10.
Kungiyar ta Arsenal ta fara zura kwallon farko ne ta hannun Santi Cazorla, kafin daga baya Aaron Ramsey ya kara kwallo ta biyu.
Kafin kuma a tashi wasan ne dan kwallon Arsenal Olivier Giroud, ya samu dama tun daga yadi na 25, ya kuma sharara kwallo ta uku a ragar Man City.
Wannan nasara dai tamkar wani karin karfin gwiwa ne ga manajan kulaf din na Arsenal Arsene Winger, gabanin wasan su na farko a gasar cin kofin Premier Ingila na kakar 2014 zuwa 2015, wanda Arsenal din za ta fara bugawa da kulaf din Crystal Palace a makon gobe.
Da yake tsokaci bayan kammalar wasan, Wenger ya ce wasan ya burge shi kwarai. Kuma 'yan wasan sa sun taka rawar gani, sun kuma taka leda yadda ya kamata a dukkanin wasan.
Wenger ya kara da cewa nasarar su ta wannan karo, za ta basu zarafin fuskantar kalubalen da ke tafe, ciki hadda na gasar Premier, wadda ya ce za su yi kokarin farawa da kafar dama.
"Wasan mu da Crystal Palace wasa ne wanda zai zamo na daban, ya kamata mu dage, muyi taka-tsantsan domin cimma nasarar da muke fatan samu." A kalaman Arsene Wenger. (Saminu Alhassan)