in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kocin Real Madrid ya ce babu sauran dan wasan gaba da za a sayo
2014-08-01 09:39:39 cri
Kocin kungiyar kwallon kafar Real Madrid Carlo Ancelotti, ya kauda rade-radin da ake yi, cewa kungiyar za ta sake kara sayo wani sabon dan wasan gaba.

A cewar Ancelotti kulaf din na sa, ya riga ya dakko dan wasan tsakiyan nan dan kasar Colombia James Rodriguez da Tony Kroos na Jamus, sai dai kasancewar Alvaro Morata ya koma Juventus daga Real Madrid din, yayin da kuma Karim Benzema ke jiyyar raunin da ya samu a gasar cin kofin duniya da aka kammala, ya sanya kulaf din kasancewa da dan gaba daya tak a halin yanzu.

A baya dai ana rade-radin Real Madrid na zawarcin Radamel Falcao daga Monaco, sai dai Ancelotti ya ce kasancewar Benzema na samun sauki, ba su da bukatar sake dakko wani sabon dan wasan gaba sabo.

Ancelotti wanda ya bayyana wannan matsayi na kulaf din sa, bayan da suka tashi wasa kunnen doki 1 da 1, da kulaf din Inter Milan a birnin California, ake kuma zargin matsawa Gareth Bale aka yi, ya buga tsakiya, ya kara da cewa, kasancewar su na da Benzema, da Isco ba sa bukatar karin wani dan wasan na gaba.

Kocin na Real Madrid wanda ya yaba da kwazon Bale bayan kammala hutun bazarar data shude, ya kuma ce suna dakon zuwan Rodriguez da suka sayo kan kudi har Euro miliyan 80.

Rodriguez dai zai isa sabon kulaf din na sa ne ran 1 ga watan Agusta mai zuwa, zai kuma kasance dan wasan kulaf Madrid mai daraja, da kankantar shekararu, wanda aka sayo musamman domin nasarar kulaf din a nan gaba.

Kaza lika zuwan Rodriguez zai fayyace makomar Angel Di Maria, wanda ya zamo dan wasan Madrid din mafi kwazo a rabin kakar wasannin da ta gabata, ya kuma taka rawar gani a gasar cin kofin duniya ga kasar sa ta Argentina, kafin ya samu rauni a gasar.

A hannu guda kuma ana rade-radin PSG da Manchester United na burin daukar daya daga 'yan wasan Real Madrid, wanda ke son barin kulaf din. Lamarin da wasu ke ganin wata kila ya na da alaka da Di Maria, ko da yake dai kocin Madrid din ya ce bai san wannan batu ba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China