in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kocin Barca ya ce akwai yiwuwar kara sayen sabbin 'yan wasa
2014-08-20 16:58:29 cri
Kocin FC Barcelona Luis Enrique ya ce har yanzu akwai damar kara shigo da wasu kwararrun 'yan wasa cikin kulob dinsa kafin karshen watan Agustan nan, duk da cewa ya zuwa yanzu kulob din ya cika da 'yan wasa sababbin jini masu yawa.

Tuni dai filin wasan kulob din na Barcelona ya riga ya ga zuwan masu tsaron gida 2, wato su Ter Stegen da Claudio Bravo, da 'yan wasan baya 2, wato su Jeremy Mathieu da Thomas Vermaelen, da 'yan wasan tsakiya Ivan Rakitic da Luis Suarez, wadanda dukkansu aka kulla kwagila tare da su a wannan lokaci na zafi.

Sai dai duk da hakan a wannan lokaci da ake dab da bude gasar La-Liga ta kasar Spaniya, kocin na Baca Luis Enrique ya ce akwai yiwuwar kara shigowar sabbin 'yan wasa cikin kulaf din.

Yayin hirar sa da manema labaru, Luis ya ce kulob din sa na kokarin bincikar kasuwannin kasashe daban daban, don neman samun karin kwararrun 'yan wasa wadanda za su iya karfafa kwarin gwiwar kulob din na sa.

Game da tabbatar da hukuncin nan da wata kotun wasanni ta yanke kan Suarez na hana shi shiga wasanni har tsawon watanni 4 kuwa, sakamakon cizon dan wasan bayan kasar Italia Giorgio Chiellini da ya yi, lokacin gasar cin kofin duniya da ta gudana a Brazil, Luis ya ce hakan ba zai dami kungiyar ta sa ba, duba da yadda ta riga ta cika da kwararrun 'yan wasa masu yawa, wadanda za su iya taka rawar gani da zarar an fara taka leda a gasar ta La-Liga.

Haka zalika Luis ya bayyana dalilin da ya sa shi baiwa kungiyar kwallon kafar Sevilla bashin matashin dan wasan sa Gerard Deulofeu, a cewar Luis, dan wasan ba zai samu isashiyar dama da yake bukata a Bacalona ba a wannan lokaci, don haka abu ne da ya dace gare shi ya samu damar kara gogewa a wani kulaf din na daban.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China