Sanarwar ta bayyana cewa, Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da yadda aka saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta wucin gadi a zirin Gaza wadda wa'adinta zai kare a daren ranar 19 ga wata, kana ya nuna bakin ciki kan rikicin da aka kara samu a tsakanin Palesdinu da Isra'ila, tare da kashedi cewa, kasashen biyu su ke da alhakin magance tsanatar hali.
Hakazalika kuma, sanarwar ta ce, an dogara kan shawarwarin da aka yi a birnin Alkahira na kasar Masar wajen samar wa jama'ar dake zirin Gaza makoma mai kyau da kuma samar da zaman lafiya na dogon lokaci ga jama'ar Isra'ila.
Don haka Ban Ki-moon ya yi kira ga Palesdinu da Isra'ila da su yi kokarin biyan bukatun jama'arsu ta hanyar hanzarta cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta na dogon lokaci. (Zainab)