Madam Hua ta bayyana hakan ne yau Alhamis yayin da shugaban Amurka Barack Obama ya lashi takwabin kaddamar da hari ta sama a kasashen Iraki da Syria inda ta ce, kamata ya yi a martaba dokokin kasa da kasa game da yaki da ta'addanci.
Hua ta ce, yakin da ake da ayyukan ta'addanci a duniya a halin yanzu batu ne mai sarkakiya, don haka take fatan kasashen duniya za su hada kai da kasashe da abin ya shafa a kokarin da suke na dawo da doka da oda cikin hanzari da sulhuntawa, zaman lafiya da ci gaban.
Ta ce, wannan mataki zai taimaka wajen kawar da karuwar ayyukan ta'addanci a wadannan wurare ta yadda za a samu dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar.
Madam Hua ta ce, kasar Sin a shirye take ta martaba ka'idar mutunta juna, nuna daidaici da hadin kai don karfafa hadin gwiwar yaki da ta'adanci tare da sauran kasashen duniya da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya. (Ibrahim)