Gong Xiaosheng ya ce, Mr Wang Yi ya bayyana ra'ayin kasar Sin na sa himma wajen shiga ayyukan hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa kan yaki da ta'addanci, kana ya sanar da matsayin da Sin ke dauka kan wannan batu, wato tilas ne a bi dokokin duniya da ka'idojin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa yayin da ake yaki da ta'addanci. Haka kuma bin kundin tsarin mulkin MDD da kudurin kwamitin sulhu yayin da ake daukar matakai, wannan matsayin da ya dace da ra'ayoyin kasa da kasa kan batun.
Daga nan sai, Gong Xiaosheng ya jaddada cewa, yanzu kasa da kasa sun dora muhimmanci sosai kan tinkarar barazanar ta'addanci, yana fatan za su iya aiwatar da hakikan ayyuka. A nata bangaren kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace da kuma shiga hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa kan yaki da ta'addanci. (Zainab)