Rahotanni daga rundunar 'yan sanda a lardin Xinjiang mai cin gashin kan sa dake arewa maso yammacin kasar Sin, na cewa, wani hari da wasu 'yan ta'adda suka kaddamar a ranar Litinin, ya janyo salwantar rayukan mutane, tare da jikkatar wasu da dama.
An ce, maharan rike da wukake sun aukawa caji ofis din 'yan sanda, da kuma wasu gine-gine gwamnati a garin Elixku, yayin da wasunsu suka kai hari ga garin Huangdi, a gundumar Shache dake yankin Kashgar. Har wa yau maharani sun rika farma fararen hula, tare da barnata ababen hawa ba kakkautawa.
Daga bisani dai 'yan sanda su bude wuta, lamarin da nan take ya janyo mutuwar da dama daga maharan.
Kaza lika bayanan da rundunar 'yan sandan yankin ta fitar sun nuna cewa, harin ya ritsa da mazauna yankin 'yan kabilar Uygur da na Han, baya ga motoci 31 da maharani suka barnata.
Tuni dai jami'an tsaro suka fara gudanar da bincike kan lamari, ko da yake dai sun bayyana harin a matsayin wani aikin ta'addanci, da wasu bata gari suka shirya kafin aiwatar da shi. (Saminu)