in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Botswana na shirin daukar tsauraran matakai a kasafin kudin shekara ta 2013
2013-02-05 14:06:45 cri
Ministan kudi na kasar Botswana Kenneth Matambo, ya fada a ranar Litinin cewa, kasar ta yi shirin daukar tsauraran matakai game da kudaden da gwamnati ke kashewa, da nufin daidaita kasafin kudin kasar na 2013 sakamakon rashin tabbas dangane da makomar tattalin arzikin kasar da na duniya baki daya.

Kenneth Matambo ya ce, an samu rarar kudin kasar Pula miliyan 779 kimanin dala miliyan 96.2, wato kimanin kashi 0.6 cikin 100 na GDP din kasar a ayyukan da gwamnatin za ta gudanar a shekarar kudi ta 2013-2014.

Matambo ya ce, za a dauki matakan tsuke bakin aljihu saboda rashin tabbas din da ke ci gaba da shafar tattalin arzikin duniya.

Ministan ya ce, Botswana na son dawo da ci gaban kasar da hangen nesan gwamnati na bunkasuwar tattalin arziki na kashi 5.9 cikin 100 a shekara ta 2013, yayin da a shekara ta 2012 ya yi hasashen kasar za ta samu cigaban kashi 4.4 cikin 100.

Kasar ta Botswana ta yi kokarin cike gibin da kasar ta samu a shekaru uku da suka gabata sakamakon matsalar tattalin arzikin duniya a shekara ta 2008 lamarin da ya durkusar da tattalin arzikin kasar mai arzikin lu'u-lu'u.

An danganta wannan koma baya ga tsauraran matakan da aka dauka, daya daga cikin manyan ayyukan tattalin arzikin kasar.

A cewar ministan, shekarar kudi ta 2012/2013 ta kasance shekarar farko da kasar ta samu rarar kasafin kudi tun shekara ta 2009, inda ta samu kudin shiga da jari da ya kai kudin kasar Pula biliyan 41.91 yayin da adadin kudaden da gwamnati ta kashe da wanda ta bayar rance suka kai kudin kasar Pula biliyan 41.08.

Baki daya, kasafin kudin kasar na shekara ta 2012/13 ya nuna cewa, an samu rarar Pula miliyan 835 idan aka kwatanta da Pula biliyan 1.15 cikin ainihin kasafin kudin da aka tsara tun farko. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China