in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Botswana na bukatar yin tazarce a karo na biyu
2014-09-23 15:08:57 cri
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Botswana ya bayar a ranar 22 ga wata, an ce, babban kotun kasar ta amince da rokon shiga takarar neman shugabancin kasar da shugaban kasar na yanzu Ian Khama ya gabatar.

Khama da sauran 'yan takara biyu wato dan jam'iyyar BCP Gilson Saleshando da kuma dan jam'iyyar BDP, Duma Boko za su fafata a zaben shugaban kasar da za a shirya a watan Oktoba.

Za a gudanar da zaben kasar a ranar 24 ga watan Oktoba na bana, kuma za a zabi membobin majalisar dokokin kasar 57 da membobin majalisar dokokin jihohin kasar 490. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China