A gun taron manema labaru da aka gudanar a birnin Gaborone dake kasar Botswana a wannan rana, Masisi ya bayyana cewa, a karshen watan Yuni, wani rukunin yaki da talauci dake karkashin jagorancinsa ya kai ziyara kasar Sin da Indiya. Rukunin ya yi bincike kan ayyukan yaki da talauci a kasashen biyu, da kuma yin mu'amala tare da manyan jami'an kasashen biyu masu kula da ayyukan yaki da talauci. Ya ce, ayyuka da nasarorin da gwamnatin kasar Sin ta samu wajen yaki da talauci sun burge shi sosai, kasarsa tana son koyon fasahohin Sin a fanonin yaki da talauci ta hanyar kimiyya da fasaha da kara aiwatar da manufofin gwamnati kan mutane masu fama da talauci da dai sauransu.
Jakadan Sin dake kasar Botswana Liu Huanxing wanda ya halarci taron manema labarun ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta samu nasarori da dama wajen kawar da talauci a shekaru fiye da 10 da suka gabata, amma duk da haka tana fuskantar kalubale a wannan fanni. A halin yanzu, kasar Sin babbar kasa ta biyu ce mai karfi tattalin arziki a duniya, amma bisa ma'aunin talauci na MDD, al'ummar Sin fiye da miliyan 100 suna fama da talauci. Yadda za a rage yawan mutanen da ke fama da talauci yayin da ake raya tattalin arzikin kasar shi ne babban kalubalen da kasar Sin ke fuskanta.(Zainab)