in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dole kasashen duniya su dauki matakin dakatar da Ebola cikin sauri
2014-10-09 10:39:06 cri

Dole ne gamayyar kasa da kasa ta gaggauta sa niyya da tashi tsaye domin dakatar da annobar cutar Ebola a kasashen Afrika da matsalar ta fi shafa, in ji karamin sakatare janar, kana shugaban tawagar aikin gaggawa ta MDD domin yaki da wannan annoba, Anthony Banbury a yayin wani taron manema labarai a ranar Laraba.

A cewarsa, matsalar kiwon lafiya ta zazzabin Ebola dake shafar wadannan kasashen Afrika na da sarkakiya sosai, kuma tana bukatar kokarin kulawar da gwamnatocin kasa da kasa, da abokan huldar cigaba, da MDD da kuma kungiyoyi masu zaman kansu ke yi cikin hadin gwiwa.

Jami'in na ganin matsalar cutar ba kawai tana shafar bangaren kiwon lafiya ba, har ma da bangaren ilimi, noma da cigaba cikin gida daga tushe. A yayin rangadinsa na aiki a Guinea, mista Banbury ya samu tattaunawa tare da shugaban kasar Alpha Conde, da kwamitin ministoci kan daidaita matsalar, da kwamitin kasa na yaki da cutar Ebola, da kuma abokan arzikin kasar Guinea. Misata Banbury ya jaddada wa gwamnatin Guinea da tallafin kayayyaki da taimakon kudi na tsarin MDD kan yaki da cutar Ebola, domin MDD tana kwarewa sosai kan daidaita matsalolin kiwon lafiya. Bisa kokarin shiga gaba kan ayyukan MDD a kasar, za'a nada wani wakilin da zai wakiltar babban sakatare na MDD Ban Ki-moon a 'yan kwanaki masu zuwa a Guinea, ta yadda zai iya aiki tare da gwamnatin Guinea da sauran bangarorin dake wannan kasa.

Matsalar kiwon lafiya a yammacin Afrika ita kadai ce da ba a taba ganin irinta a tarihi, kuma duniya ba ta shirya ba domin fuskantar irin wannan matsala, in ji mista Banbury, kafin ya gabatar da wata mafitar yaki da cutar Ebola daga dukkan fannoni. A cewarsa, dalilin haka ne, dole kungiyoyin tsarin MDD su dauki mataki cikin sauri, tare da kara azama a kasashen da matsalar ta fi shafa, ta yadda za'a samu damar killace da hana yaduwar Ebola zuwa wasu kasashe. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China