in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi Allah wadai da kisan jami'an tawagar MDD a Mali
2014-08-19 10:33:05 cri

Kwamitin tsaron MDD ya yi Allah wadai da harin kunar bakin wake da aka kaiwa tawagar jami'an wanzar da zaman lafiya ta MDD MINUSMA a Arewacin Mali, harin da ya sabbaba rasuwar ma'aikatan biyu, tare da jikkata wasu karin mutum 7.

Wata sanarwar da mambobin kwamitin suka fitar a ranar Litinin, ta yi kira ga mahukuntan kasar Malin da su gaggauta gudanar da bincike game da wannan lamari, tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan ta'asa gaban kuliya.

Kaza lika sanarwar ta bayyana dukkanin wasu matakai daka iya yin barazana ga ma'aikatan MDD a matsayin ayyukan ta'addanci da suka saba wa doka, wadanda kuma ya wajaba a dauki dukkanin matakai karkashin dokokin MDDr wajen magance su.

Wannan lamari dai na zuwa ne bayan kammalar zagayen farko na tattaunawa tsakanin sassa masu ruwa da tsaki a kasar ta Mali, tattaunawar da sassan kasar suka gudanar a birnin Aljiers na kasar Aljeriya cikin watan Yulin da ya shude.

A baya-bayan nan lamura na sake tabarbarewa a Arewacin kasar ta Mali, bayan ci gaba da aka samu a bara, sakamakon dauki-ba-dadin da mayakan 'yan awaren Azbinawa ke yi da dakarun gwamnati, inda a ranar Asabar wasu mahara suka tashi wasu nakiyoyi da suka boye cikin wata mota, kusa da wani shingen jami'an tsaro a kauyen Ber dake Timbuktu, harin da shi ne na baya-bayan nan da aka kai kan tawagar jami'an wanzar da zaman lafiyar na MINUSMA. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China