141017-WHO-ta-jaddada-muhimmancin-taimaka-wa-kasashen-Afirka-wajen-tinkarar-cutar-Ebola-Kande.m4a
|
Ban da wannan kuma Madam Nuttall ta ce, yanzu yadda cutar Ebola ke yaduwa ya tsananta, yawan wadanda suka mutu da wadanda ka iya kamuwa da cutar zai ci gaba da karuwa. Tana mai cewa,
"An kiyasta cewa, yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar Ebola za ta zarce 4500 a wannan mako, yawan masu kamuwa da cutar kuwa zai wuce 9000. Sa'an nan kuma cutar za ta ci gaba da kawo babbar barazana ga masu aikin jiyya, kawo yanzu dai masu aikin jiyya 427 ne suka kamu da cutar, 236 daga cikinsu kuwa sun riga mu gidan gaskiya. Haka kuma bisa kididdigar da muka samu, an ce, wannan adadi zai ninka sau daya a ko wadanne makwanni hudu."
Bugu da kari, Madam Nuttall ta amince da cewa, bisa yanayin da cutar ke yaduwa a halin yanzu, akwai yiyuwar bullar cutar a wasu kasashe. Kawo yanzu dai nahiyar Afirka ne ya kamata a mai da hankali a kai, musamman ma kasashen Afirka hudu da ke makwabtaka da kasashe masu fama da cutar, wato Guinea Bissau, Senegal, Mali da kuma Cote d'Ivoire. Ban da su kuma, ya kamata a kara karfin ayyukan rigakafi a sauran kasashen Afirka 11 da ke fama da tasirin kasashe masu fama da cutar, wadanda suka hada da Benin, Kamaru, Afirka ta Tsakiya, Kongo Kinshasa, Gambia, Ghana, Mauritania, Burkina Faso, Najeriya, Sudan ta Kudu da kuma Togo. Wadannan kasashe kuwa ba su da ingantattun na'urorin kiwon lafiya, sa'an nan ba su da karfi wajen shawo kan cututtuka. Madam Nuttall ta jaddada cewa, dole ne a taimaka wa wadannan kasashe wajen yin shiri sosai don tinkarar matsalar da kuma hana yaduwar cutar Ebola. Ta kara da cewa,
"Watakila a bukaci karin lokuta ko watanni kafin a dakatar da yaduwar cutar Ebola. A sa'I daya kuma, ya kamata mu yi kokari don tabbatar da hana yaduwar cutar a sauran kasashe. Kila a gano wani mutumin da ya kamu da cutar a wasu kasashe, amma muna fatan ba za mu ga abkuwar hakan a nan gaba ba."
Madam Nuttall ta kara da cewa, WHO za ta aika da tawagar musamman zuwa wadannan yankuna, domin taimaka musu wajen tsara shirin tinkarar matsalar, da yin gwaje-gwajie, da kuma shirya isassun kayayyakin ba da kariya, ta yadda za a iya gano masu kamuwa da cutar Ebola da kuma killace su cikin lokaci.
A waje daya kuma, Madam Nuttall ta yi tsokaci cewa, akwai bambanci a tsakanin batun gano cutar Ebola a wata kasa da kuma batun yaduwar cutar a wata kasa. A kasashen da ke da kyakkyawan tsarin kiwon lafiya, yiyuwar yaduwar cutar Ebola kalilan ne. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da wadannan kasashe na da kayayyakin jiyya masu inganci, da kuma fasahohin zamani na shawo kan cututtuka,sannan suna da kwarewa wajen hana yaduwar cutar Ebola a cikinsu. Ban da wannan ta jaddada cewa, har yanzu yankin da cutar Ebola ta fi kawo barazana shi ne Afirka,don haka ya kamata a mai da hankali a kan kasashe uku da ke yammacin Afirka masu fama da cutar. (Kande Gao)