A wajen bikin sa hannu, Moustapha Koutoubou SANO, ministan hulda da kasa da kasa na kasar Guinea, ya ce muhimmancin tallafin ya dace da tunawar jama'ar kasar Guinea ta zuriyoyi daban daban.
A nasa bangaren, jakadan kasar Sin dake Guinea, mista Bian Jianqiang, ya ce kasar Sin tana ci gaba da kokarin tallafawa kasashen Afirka a kokarinsu na shawo kan cutar Ebola, inda ta kara samar da tallafin da darajarsa ta kai kudin Sin RMB miliyan 200 ga Guinea, Laberiya, Saliyo, da dai sauransu, tallafin da ya kunshi dalar Amurka miliyan 1 da abinci mai darajar dalar Amurka miliyan 2 da ta ba kasar Guinea. (Bello Wang)