Mr Bires ya bayyana cewa, babban canjin da kasar Sin za ta samu yana da nasaba da makomar kasar Sin, kana zai yi tasiri ga bunkasuwar duk duniya. Ya yi imani da cewa, sabbin shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za su ci gaba da gudanar da ayyuka cikin adalci tare da dora muhimmanci kan halin da duniya ke fuskanta a halin yanzu. A karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, Sin za ta sa lura ga halin da kasa da kasa ke ciki, sabbin manufofin da aka tsara za su bayar da muhimmanci ga aikin kiyaye zaman lafiya na duniya, da kuma sa kaimi ga kasa da kasa da su raya dangantakarsu yadda ya kamata. Yana fatan cewa, za a gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 18 yayin da ake kyautata tsarin zamantakewar al'ummar kasar, don haka sabbin shugabannin jam'iyyar za su fuskanci kyakkyawar dama tare da tunkarar kalubalen dake tafe. (Zainab)